620 B
620 B
Benaiya
Gaskiya
Benaiya sunan mutane ne da yawa a cikin Tsohon Alƙawari.
- Benaiya ɗan Yehoyida ɗaya daga cikin jarumawan Dauda ne. Ƙwararren mayaƙi ne da aka sa shi shugaban matsaran Dauda.
- Lokacin da ake naɗa Suleman sarki, Benaiya ya taimake shi tumbuke maƙiyansa. Daga bisani ya zama hafsan rundunar mayaƙan Isra'ila.
- Wasu mazaje a cikin Tsohon Alƙawari masu suna Benaiya har da Lebiyawa uku: da firist, da mawaƙi, da wani zuriyar Asaf.
(Hakanan duba: Asaf, Yehoyida, Balebi, Suleman)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 04:36
- 1 Sarakuna 01:08
- 2 Sama'ila 23:20-21