619 B
619 B
Belzebul
Gaskiya
Belzebul wani suna ne na Shaiɗan ko mugun ruhu. Wani lokaci ana rubuta shi haka "Belzebub."
- Wannan suna ma'anarsa "ubangijin ƙudaje" ma'ana "mai mulki akan mugayen ruhohi." Amma ya fi kyau a fassara wannan kalma da yadda aka rubuta ta da farko maimakon a fassara ma'anarsa.
- Za a iya fassara ta kuma haka "Belzebul mugun ruhu" domin a tabbatar ko wanene ake ambata.
- Wannan suna yana da dangantaka da sunan gunkin nan "Ba'al-zebub" na Ekron.
(Hakanan duba: aljani, Ekron, Shaiɗan)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Luka 11:15
- Markus 03:22
- Matiyu 10:25
- Matiyu 12:25