628 B
628 B
Baruk
Gaskiya
Baruk sunan mutane ne da dama a Tsohon Alƙawari.
- Wani Baruk (ɗan Zabbal) ya yi aiki da Nehemiya wajen gyara garun Yerusalem.
- Kuma lokacin Nehemiya, wani Baruk kuma (ɗan Kol-Hoze) yana ɗaya daga cikin shugabanni da suka zauna a Yerusalem bayan an gyara garunta.
- Wani Baruk daban (ɗan Neriya) mataimaki ne ga annabi Irmiya, wanda ya taimake shi cikin ayyuka iri-iri kamar su rubuta saƙonni da Allah ya ba Irmiya sa'annan ya karanta wa mutane.
(Hakanan duba: manzo, Irmiya, Yerusalem, Nehemiya, annabi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Irmiya 32:12
- Irmiya 36:04
- Irmiya 43:1-3