595 B
595 B
Bartalomiyo
Gaskiya
Bartalomiyo ɗaya ne daga cikin almajiran Yesu guda sha biyu.
- An aiki Bartalomiyo tare da sauran manzanni, su tafi su yaɗa bishara su yi al'ajibai cikin sunan Yesu.
- Yana kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka ga Yesu ya koma sama.
- Bayan 'yan sati da dama da faruwar wannan, yana tare da sauran manzanni a Yerusalem ranar Fentikos sai Ruhu Mai Tsarki ya sabko masu.
(Hakanan duba: manzo, labari mai daɗi, Ruhu Mai Tsarki, al'ajibi, Fentikos, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 01:12-14
- Luka 06:14-16
- Markus 03:17-19