764 B
764 B
Barnabas
Gaskiya
Barnabas ɗaya ne daga cikin Kiristoci na farko da suka kasance tare da manzanni.
- Barnabas Ba'isra'ile ne na kabilar Lebi kuma daga tsibirin Sifuros.
- Sa'ad da Shawulu (Bulus) ya zama Kirista, Barnabas ya matsa wa masu bada gaskiya su karɓe shi a matsayin ɗan'uwa mai gaskatawa.
- Barnabas da Bulus sun yi tafiya tare wajen yaɗa bishara mai daɗi game da Yesu cikin birane daban-daban.
- Sunansa Yosef, amma ana kiransa "Barnabas," ma'ana "ɗan ƙarfafawa."
(Hakanan duba: Kirista, Saifuros, labari mai daɗi, Lebi, Bulus)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 04:36
- Ayyukan Manzanni 11:26
- Ayyukan Manzanni 13:03
- Ayyukan Manzanni 15:33
- Kolosiyawa 04:10-11
- Galatiyawa 02:9-10
- Galatiyawa 02:13