ha_tw/bible/names/asherim.md

1.3 KiB
Raw Permalink Blame History

Ashera, ginshiƙin Ashera, ginshiƙan Ashera, Ashtoret, Ashtoretai

Gaskiya

Ashera sunan wata allahiya ce wadda mutanen Kan'ana suke mata sujada a lokacin Tsohon Alƙawari. "Ashtoret" wataƙila wani suna ne na "Ashera" ko kuma sunan wata allahiyar daban da tayi kusa da tata.

  • Wannan kalmar "ginshiƙan Ashera" ana nufin wasu sassaƙaƙƙun siffofi ne na itace ko sassaƙaƙƙun itatuwa da aka yi domin su wakilci wannan allahiya.
  • Ginshiƙan Ashera yawancin lokaci ana kafa su kusa da bagadin gunkin nan Ba'al, wanda ake tunanin shi ne mijin Ashera. Wasu jinsin mutane suna wa Ba'al sujada sun ɗauke shi allahn rana kuma Ashera ko Ashtoret allahiyar wata.
  • Allah ya umarci Isra'ilawa su lalata duk sassaƙaƙƙun siffofi na Ashera.
  • Wasu shugabannin Isra'ilawa kamar su Gidiyon, Sarki Asa, da Sarki Yosiya sun yi biyayya da Allah suka shugabanci mutane a lallatar da waɗannan gumaku.
  • Amma wasu shugabannin Isra'ilawa kamar Sarki Suleman, Sarki Manasse, da Sarki Ahab basu kawar da ginshiƙan Ashera ba amma suka iza mutane su yiwa waɗannan gumaku sujada.

(Hakanan duba: allahn ƙarya, Ba'al, Gidiyon, siffa, Suleman)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 18:04
  • 2 Sarakuna 21:03
  • Ishaya 27:9
  • Littafin Alƙalai 03:7-8
  • Mika 05:14