535 B
535 B
Asha
Gaskiya
Asha ɗan Yakubu na takwas ne. Zuriyarsa tana ɗaya daga cikin kabilu sha biyu na Isra'ila wanda kuma ake kira "Asha."
- Mahaifiyar Asha ita ce Zilfa, baranyar La'aitu.
- Ma'anar sunansa "farinciki, ko "mai albarka."
- Asha kuma sunan yankin ƙasar da aka ba kabilar Asha ne lokacin da Isra'ilawa suka shiga ƙasar alƙawari.
(Hakanan duba: Isra'ila, kabulu sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 02:1-2
- 1 Sarakuna 04:16
- Ezekiyel 48:1-3
- Farawa 30:13
- Luka 02:36-38