718 B
718 B
Ashdod, Azotus
Gaskiya
Ashdod ɗaya daga cikin shahararrun birane biyar na Filistiyawa ne. Ashdod na kudu maso yamma da Kan'ana kusa da Tekun Baharmaliya, dai-dai rabin tafiya tsakanin biranen Gaza da Yoffa.
- Haikalin gunkin allahn Filistiyawa Dagon a Ashdod yake.
- Allah ya hukunta mutanen Ashdod ainun da Filistiyawa suka sace akwatin alƙawari suka aje shi a haikalin tsafinsu a Ashdod.
- Da Girik sunan birnin nan Azotus ne. Yana ɗaya daga cikin biranen da mai wa'azi, Filib ya shaida masu bishara.
(Hakanan duba: Ekron, Gat, Gaza, Yoffa, Filibiya, Filistiyawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sama'ila 05:1-3
- Ayyukan Manzanni 08:40
- Amos 01:8
- Yoshuwa 15:45-47
- Zakariya 09:06