876 B
876 B
Atazazas
Gaskiya
Atazazas sarki ne da ya yi sarauta bisa ƙasar Fasiya daga misalin 464 zuwa 424 BC.
- A mulkin Atazazas, Isra'ilawa daga Yahuda suna bautar talala a Babila wadda take ƙarƙashin mulkin Fasiya a lokacin.
- Atazazas ya yaddar wa Ezra firist da wasu shugabannin Yahudawa su bar Babila su koma Yerusalem su koya wa Isra'ilawa Shari'ar Allah.
- Daga baya a wannan lokaci, Atazazas ya yardar wa Nehemiya mai ƙoƙon shayarwarsa a fãda ya koma Yerusalem ya bida Yahudawa domin a sake gina garu kewaye da birnin.
- Saboda Babila tana ƙarƙashin mulkin Fasiya, Atazazas wani lokaci ana kiransa "sarkin Babila."
- A lura cewa Atazazas daban yake da Zazas (Ahasurus).
(Hakanan duba: Ahasurus, Babilon, mai ƙoƙon shayarwa, Ezra, Nehemiya, Fasiya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ezra 04:7-8
- Ezra 07:1-5
- Nehemiya 02:01
- Nehemiya 13:6-7