ha_tw/bible/names/antioch.md

1.1 KiB
Raw Permalink Blame History

Antiyok

Gaskiya

Antiyok sunan garuruwa biyu ne a Sabon Alƙawari. Daya na Siriya kusa da bakin ruwan da ake ce da shi Tekun Baharmaliya. Dayan yana Roma ne a lardin Fisidiya, kusa da birnin Kolossiya.

* Wata ƙaramar ikilisiya a Antiyok ta Siriya ita ce wurin da aka fara kiran masu gaskatawa da Yesu "Kiristoci." Wannan coci tana da himmar aika masu bishara wajen Al'ummai.

  • Shugabannin ikilisiyar Yerusalem suka aika da wasiƙa zuwa ga masu bada gaskiya a iklisiya ta Antiyok a Siriya domin su taimake su su sani ba sa buƙatar su bi dokokin Yahudawa kafin su zama Kirista.
  • Bulus da Barnabas da Yahaya Markus suka tafi Antiyok a Fisidiya su yi bishara. Wasu Yahudawa daga wasu biranen suka zo suka tada hargitsi da ƙoƙarin su kashe Bulus. Amma mutane da yawa, Yahudawa da Al'ummai suka saurari koyarwar kuma suka gaskata da Yesu.

(Hakanan duba: Barnabas, Kolosse, Yahaya Markus, Bulus, lardi, Roma, Siriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 03:10-13
  • Ayyukan Manzanni 06:5-6
  • Ayyukan Manzanni 11:19-21
  • Ayyukan Manzanni 11:26
  • Galatiyawa 02:11-12