660 B
660 B
Andarawus
Gaskiya
Andarawus yana ɗaya daga cikin mutum goma sha biyu da Yesu ya zaɓa su zama almajiransa na kurkusa da shi {daga baya an kira su manzanni}.
- Dan 'uwan Andarawus shi ne Siman Bitrus. Dukkan su biyu masunta ne.
- Da Bitrus da Andarawus suna kamun kifi ne a Tekun Galili sa'ad da Yesu ya kiraye su su zama almajiransa.
- Kafin Bitrus da Andarawus su gamu da Yesu, sun yi almajiranci a wajen Yahaya Mai yin Baftisma.
(Hakanan duba: manzo, almajiri, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 01:12-14
- Yahaya 01:40
- Markus 01:17
- Markus 01:29-31
- Markus 03: 17-19
- Matiyu 04:19
- Matiyu 10:2-4