657 B
657 B
Ahab
Gaskiya
Ahab mugun sarki ne wanda ya yi mulki bisa masarautar arewa ta Isra'ila daga 875 zuwa 854 BC.
- Sarki Ahab ya sa mutanen Israr'ila suka yi sujada ga gumaku.
- Annabi Iliya ya fuskanci Ahab ya gaya masa za a yi mugun fari shekara uku da wata shida sakamakon hukuncin zunuban da Ahab ya sa Isra'ila ta aikata.
- Ahab da matarsa Yezebel sun yi waɗansu mugayen abubuwa da yawa, har ma da amfani da ikon da suke da shi su kashe mutane marasa laifi.
(Hakanan duba: Ba'al, Iliya, Yezebel, masarautar Isra'ila, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 18:1-2
- 1 Sarakuna 20:1-3
- 2 Tarihi 21:06
- 2 Sarakuna 09:08