788 B
788 B
Abiya
Gaskiya
Abiya sunan wani sarki ne na Yahuda wanda ya yi mulki daga 915-913 BC. Ɗan Sarki Rehobowam ne. Akwai wasu mutane kuma da dama da ake kiran su Abiya a cikin Tsohon Alƙawari.
- 'Ya'yan Sama'ila maza Abiya da Yowel shugabanni ne bisa mutanen Isra'ila a Biyasheba. Saboda Abiya da ɗan'uwansa sun yi rashin gaskiya da haɗama, mutane suka roƙi Sama'ila ya naɗa masu sarki da zai yi mulki a kansu.
- Wani Abiya ɗaya ne daga cikin firistocin haikali a zamanin Sarki Dauda.
- Abiya sunan ɗaya daga cikin 'ya'ya maza na Sarki Yerobowam ne.
- Abiya kuma sunan wani babban firist ne da ya dawo Yerusalem tare da Zerubabel daga bautar talala a Babila.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 15:03
- 1 Sama'ila 08:1-3
- 2 Tarihi 13:19
- Luka 01:05