610 B
610 B
Haruna
Gaskiya
Haruna wan Musa ne. Allah ya zaɓi Haruna ya zama babban firist na farko domin mutanen Isra'ila.
- Haruna ya taimaki Musa a wajen yiwa Fir'auna magana ya saki Isra'ilawa su tafi 'yantattu.
- Sa'ad da Isra'ilawa ke tafiya cikin jeji, Haruna ya yi zunubi ta wurin ƙera wa mutane gunki domin suyi masa sujada.
- Allah kuma ya zaɓi Haruna da zuriyarsa su zama (firist) firistoci domin mutanen Isra'ila.
(Hakanan duba: firist, Musa, Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 23:14
- Ayyukan Manzanni 07:38-40
- Fitowa 28:1-3
- Luka 01:05
- Littafin Lissafi 16:45