899 B
899 B
sujada
Ma'ana
Yin "sujada" na nufin a girmama, yabo da kuma yin biyayya ga wani, musamman Allah.
- Wannan kalmar a zahiri na nufin "durkusawa ƙasa" ko " mutum ya rusuna da fuskansa ƙasa" domin girmama wani.
- Muna yin sujada ga Allah sa'ad da muke bauta masa da kuma girmama shi, ta wurin yi masa yabo da yi masa biyayya.
- Sa'ad da Isra'ilawa ke yiwa Allah sujada, sukan yi hadayar dabbobi a bisa bagadi.
- Wasu na yiwa allolin ƙarya sujada.
Shawarwarin Fassara:
- Kalmar "sujada" za a iya fassarawa a matsayin "rusunawa ƙasa ga" ko "girmamawa da hidima" ko "girmamawa da biyayya."
- Wasu nassosin, za a iya fassarawa a matsayin "yabo mai tawali'u" ko "bayar da girmamawa da yabo."
(Hakanan duba: hadaya, yabo, girmamawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Kolosiyawa 02:18-19
- Maimaitawar Shari'a 29:18
- Fitowa 03:11-12
- Luka 04:07
- Matiyu 02:02
- Matiyu 02:08