1.3 KiB
1.3 KiB
mai hikima, hikima
Ma'ana
Kalmar "hikima" na bayyana wani ne da ya fahimci abin dake dai-dai na gari abin yi ya kuma aikata. "Hikima" fahimta da kuma aikata abin da ke gaskiya ne da kuma abin da ke dai-dai.
- Zama mai hikima ya ƙunshi ɗaukar matakai, musamman zaɓen a aikata abin da zai farantawa Allah rai.
- A Littafi Mai Tsarki, kalmar "hikimar duniya" ana amfani da ita a bayyana abin da mutanen duniya ke tunanin shi ne hikima, amma alhali kuwa wawanci ne.
- Mutane na zama masu hikima ta wurin sauraron Allah su kuma aikata nufinsa cikin biyayya.
- Mutum mai hikima zai nuna 'ya'yan Ruhaniya a cikin rayuwarsa, kamar farinciki, nagarta, ƙauna da hakuri.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta da nassin, wasu hanyoyin fassara "mai hikima" zasu haɗa da "biyayya ga Allah" ko "hankali da biyayya" ko "tsoron Allah."
- "Hikima" za a iya fassarata da kalma ko faɗar dake da ma'anar "rayuwar hikima" ko "rayuwar hankali da biyayya" ko "nagartaccen hukunci."
- Zaifi kyau a fassara "mai hikima" da "hikima" ta yadda zasu kasance kalmomi daban da wasu kalmomi masu muhimmanci kamar su adali ko mai biyayya.
(Hakanan duba: yi biyayya, 'ya'yan itace)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 06:03
- Kolosiyawa 03:15-17
- Fitowa 31:06
- Farawa 03:06
- Ishaya 19:12
- Irmiya 18:18
- Matiyu 07:24