1.1 KiB
1.1 KiB
karya doka, ana karya doka, an karya doka
Ma'ana
"Karya doka" na ma'anar a karya shari'a ko a keta hakkin wani taliki. "Karya doka" na nufin aikata aikin "karya doka."
- Karya doka na iya nufin keta ɗabi'a ko shari'ar hukuma ko zunubin da aka yi gãba da wani.
- Wannan kalma na da dangantaka da kalmomin "zunubi," da "laifi," musamman idan suna dangantaka da rashin biyayya da Allah.
- Dukkan zunubai karya doka ne gãba da Allah.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta da nassin, a "karya doka gãba da" za a iya fassarawa haka "yin zunubi gãba da" ko a "karya sharaɗi."
- Zai iya kasancewa wasu yarurrukan suna da faɗar haka "a gitta layi" da za a iya amfani da shi a fassara "karya doka."
- Ayi la'akari da yadda ma'anar wannan kalma ta yi dai-dai da nassin dake kewaye da Littafi Mai Tsarki sai kuma a kwatanta ta da kalmomin dake da ma'ana shigen iri ɗaya kamar su "laifi" da "zunubi."
(Hakanan duba: rashin biyayya, lalata, zunubi, laifi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sama'ila 25:28
- 2 Tarihi 26:16-18
- Kolosiyawa 02:13
- Afisawa 02:01
- Ezekiyel 15:7-8
- Romawa 05:17
- Romawa 05:20-21