1.5 KiB
1.5 KiB
haikali
Ma'ana
Haikali gini ne dake kewaye da katangaggun harabai inda Isra'ilawa suke zuwa suyi addu'a su kuma miƙa hadayu ga Allah. Yana bisa Tsaunin Moriya a cikin birnin Yerusalem.
- Yawanci kalmar "haikali" yana nufin harabar haikalin gabaɗaya, duk da harabun dake kewaye da ainihin ginin. Wasu lokutan yana nufin ginin kaɗai.
- Ginin haikalin nada ɗakuna biyu, Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki.
- Allah na nuna haikalin a matsayin wurin zamansa.
- Sarki Suleman ya gina Haikalin a zamanin mulkinsa. Ya kamata ya zama wurin sujada na din-dindin a Yerusalem.
- A Sabon Alƙawari, kalmar "haikalin Ruhu Mai Tsarki" ana amfani da ita da nufin masu bin Yesu a matsayin ƙungiya, saboda Ruhu Mai Tsarki na zama cikin su.
Shawarwarin Fassara:
- Yawanci idan nassi ya ce mutane na "cikin haikali," yana nufin harabun dake waje da ginin. Za'a iya fassara wannan haka "cikin harabun haikali" ko "cikin harabar haikalin."
- Inda yake nufin ainihin ginin kai, wasu juyin sun fassara "haikali" a matsayin "ginin hajkali," domin a bayyana nassin sosai.
- Hanyoyin da za a fassara "haikali" zasu haɗa da, "gidan Allah mai tsarki" ko "wurin sujada mai tsarki."
- Yawanci a cikin Littafi Mai Tsarki, haikali na nufin "gidan Yahweh" ko "gidan Allah."
(Hakanan duba: hadaya, Suleman, Babila, Ruhu Mai Tsarki, haraba, Sihiyona, gida)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 03:02
- Ayyukan Manzanni 03:08
- Ezekiyel 45:18-20
- Luka 19:46
- Nehemiya 10:28
- Zabura 079:1-3