1.5 KiB
1.5 KiB
rumfar sujada
Ma'ana
Rumfar sujada rumfa ce ta musamman da Isra'ilawa ke yiwa Allah sujada cikin shekaru 40 da suka yi tafiya a jeji.
- Allah ya ba Isra'ilawa umurnai domin ginin wannan babbar rumfar, wadda ke da ɗakuna biyu kuma tana zagaye da labule.
- Duk sa'ad da Isra'ilwa suka matsa zuwa wani wuri a cikin dajin domin su zauna, sai firistoci su ɗauki rumfar sujadar zuwa sansanin suna gaba. Sai su sake shirya ta a tsakiyar sabon sansaninsu.
- An yi rumfar sujadar da Itace aka zagaye ta da labulai da akayi da sutura, gashin akuya, da fatun dabbobi. tsakiyarta sun kewaye ta an kuma rufeta da labule.
- Sassan rumfar sujadar guda biyu sune wuri mai tsarki (inda bagadin ƙona turare yake) da kuma wuri mafi tsarki (inda Akwatin Alƙawari yake).
- Tsakiyar rumfar sujadar na da bagadi na ƙona hadayar dabbobi da kuma wasu tasoshi na musamman don tsarkakewa.
- Isra'ilawa suka daina amfani da rumfar sujada lokacin da aka gina haikali a Yerusalem ta hannun Suleman.
Shawarwarin Fassara:
- Kalmar "rumfar sujada" na nufin "wurin zama". Wasu hanyoyin fassara shi kuma zai iya zama "wuri mai tsarki" ko "rumfa inda Allah yake" ko "rumfar Allah."
- A tabbatar cewa fassarar wannan kalmar ta banbanta da fassarar "haikali."
(Hakanan duba: bagadi, bagadin ƙona turare, akwatin alƙawari, haikali, rumfar taruwa)
Wuraren da ake samusa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 21:30
- 2 Tarihi 01:2-5
- Ayyukan Manzanni 07:43
- Ayyukan manzanni 07:45
- Fitowa 38:21
- Yoshuwa 22:19-20
- Lebitikus 10:16-18