864 B
864 B
majami'a
Ma'ana
Majami'a gini ne inda mutanen Yahuda ke taruwa tare su yi sujada ga Allah.
- Tun zamanin dă, hidimomi a majami'a sun haɗa da lokacin addu'a, karatun maganar Allah, da koyarwa daga maganar Allah.
- Da fari yahudawa sun fara gina majami'a ne a matsayin wurin addu'a da bautar Allah a garuruwansu, domin da yawansu na zama a wurare masu nisa da haikali a Yerusalem.
- Yesu ya yi ta koyarwa a majami'u da kuma warkar da mutane a can.
- Kalmar "majami'a" anyi amfani da ita da yawa da nufin nuna tattaruwar mutane wuri ɗaya.
(Hakanan duba: warkaswa, Yerusalem, Bayahude, addu'a, haikali, maganar Allah, sujada)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 06:09
- Ayyukan Manzanni 14:1-2
- Ayyukan Manzanni 15:21
- Ayyukan Manzanni 24:10-13
- Yahaya 06:59
- Luka 04:14
- Matiyu 06:1-2
- Matiyu 09:35-36
- Matiyu 13:54