1.2 KiB
1.2 KiB
rai, rayuka
Ma'ana
Rai shine abin da ba a gani, na cikin mutum, yana nufin ɓangaren da ba jiki ba na cikin mutum.
- Wannan kalma "rai" da "ruhu" na iya zama abubuwa biyu daban, ko sukan iya zama abu biyu dake nufin abu guda.
- Idan mutum ya mutu, ransa yakan bar jikinsa.
- Kalmar "rai" wani lokacin akan yi amfani da ita akai akai ana nufin dukkan mutum. A misali, "ran da ya yi zunubi" na nufin "mutumin da ya yi zunubi" da "rai na ya gaji" na nufin, "na gaji."
Shawarwarin Fassara:
- Kalmar "rai" akan iya fassara ta da "can ciki wani" ko "mutumin dake ciki."
- A waɗansu nassosin, "rai na" ana fassara wa da "NI" ko "Ni".
- Sau da yawa kalmar "rai" akan fassara ta da "talikin" ko "shi" ya danganta da wurin da kalmar take.
- Waɗansu yarurrukan kan iya samun kalma ɗaya domin "rai" da "ruhu".
- A cikin Ibraniyawa 4:12, an raba wannan kalmar "rai da ruhu" suna nufin "zuzzurfan nutsewa ko fayyace mutumin ciki."
(Hakanan duba: ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Bitrus 02:08
- Ayyukan Manzanni 02:27-28
- Ayyukan Manzanni 02: 41
- Farawa 49:06
- Ishaya 53:10-11
- Yakubu 01:21
- Irmiya 06:16-19
- Yona 02:7-8
- Luka 01:47
- Matiyu 22:37
- Zabura 019: 07
- Wahayin Yahaya 20:4