1.5 KiB
1.5 KiB
'ya'yan Allah, yaran Allah
Ma'ana
Kalmar "'ya'yan Allah" kalma ce da aka yi ta amfani da ita tana kuma da ma'anoni da yawa.
- A Sabon Alƙawari, kalmar "'ya'yan Allah" na nufin dukkan masu bada gaskiya ga Yesu an kuma fassara ta da "yaran Allah" tun da ya kunshi maza da mata.
- Amfani da wannan kalma na nuna dangantaka da Allah kamar yadda dangantaka tsakanin ɗan mutane da ubansa take, da kuma dukkan damar da take ta samun zama 'ya'ya.
- Waɗansu mutane kan fassara kalmar "'ya'yan Allah" da aka samu a cikin Farawa 6 da mala'ika da suka faɗi - miyagun ruhohi ko iskokai. Waɗansu kuma sukan yi tunanin ikon siyasa na masu mulki ko kuma zuwa zuriyar Shitu.
- A Sabon Alƙawari, kalmar "'ya'yan Allah" na nufin dukkan masu bada gaskiya cikin Yesu kuma ana fassara shi da "'ya'yan Allah" tun da ya ƙunshi maza da mata.
- Amfani da wannan kalmar na nuna dangantaka da Allah da take kamar dangantakar 'ya'ya da mahaifinsu, da kuma dukkan damar kasancewa 'ya'ya.
- Laƙabin "Ɗan Allah" abu ne na daban: yana nufin Yesu, wanda yake maɗakaicin Ɗan Allah.
Shawarwarin Fassara:
- Inda "'ya'yan Allah" ana nufin masu bi cikin Yesu, za a iya fassara shi da "'ya'yan Allah"
- A cikin Farawa 6:2 da 4 hanyoyin fassara "'ya'yan Allah" sun haɗa da " mala'iku" "ruhohi." "shugaban dukkan halittu, ko "aljanu."
- A ƙara kuma ganin sashen "ɗa."
(Hakanan duba: mala'ika, aljani, ɗa, Ɗan Allah, mai mulki, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Farawa 06:02
- Farawa 06:04
- Ayuba 01:06
- Romawa 08:14