ha_tw/bible/kt/sonofgod.md

1.4 KiB
Raw Permalink Blame History

Ɗan Allah, Ɗa

Ma'ana

Kalmar "Ɗan Allah" na magana akan Yesu, Kalmar Allah, wanda ya zo duniya a matsayin, mutum. An kuma sha faɗinsa da "Ɗa."

  • Ɗan Allah na da siffa ɗaya da Allah Uba, kuma shi Allah ne cikkake.
  • Allah Uba, Allah Ɗa, da Allah Ruhu Mai Tsarki dukkan su ɗaya ne.
  • Ba kamar 'ya'yan mutane ba, Ɗan Allah a kodayaushe yana nan.
  • Tun daga farko, Ɗan Allah ya kasnce cikin hallitar duniya, tare da Uba da Ruhu Mai Tsarki.

Domin Yesu Ɗan Allah ne, ya ƙaunaci da kuma biyayya da Ubansa, kuma Ubansa yana ƙaunarsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Don kalmar "Ɗan Allah", ita ce mafi dacewa da fassarar "Ɗa" dai-dai da kalmar da yare ke amfani da ita wajen yin nuni da ɗan mutum.
  • A tabbatar kalmar da aka mora warin fassara "ɗa" ta zo dai-dai da wadda aka mora wurin fassara "Uba" domin waɗannan kalmomin sune kalmomi na gaske da za su iya bada gaskiyar dangantakar dake tsakanin Uba da ɗa a wannan aikin.
  • Ta amfani da babban baƙi a "Ɗa" na iya taimakawa a gane cewa ana magana ne akan Allah.
  • Kalmar "Ɗa" ita ce a takaicen "Ɗan Allah," masamman inya fita a layi guda da "Uba."

(Hakanan duba: Almasihu, kaka, Allah, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, ɗa, 'ya'yan Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 04:10
  • Ayyukan Manzanni 09:20
  • Kolosiyawa 01:17
  • Galatiyawa 02:20
  • Ibraniyawa 04:14
  • Yahaya 03:18
  • Luka 10:22
  • Matiyu 11:27
  • Wahayin Yahaya 02:18
  • Romawa 08:29