1.1 KiB
1.1 KiB
warewa daban
Ma'ana
Kalmar "warewa da ban" na nufin warewa daga wani abu domin wani dalili. Kuma "warewa daban" waɗansu mutane ko wani abu na nufin a ware su " da ban".
- Isra'ilawa an ware su domin bautar Yahweh.
- Ruhu Mai Tsarki ya umarci kiristoci a Antiyok su ware Bulus da Barnabas domin aikin da Yahweh yake so suyi.
- Mai bi wanda ya "ware" don hidima ga Yahweh an ware shi ne domin cika nufin Yahweh.
- Ɗaya daga cikin ma'anar "tsarki" shi ne a keɓe a matsayin kayan Yahweh a kuma ware daga hanyar zunubi ta duniya.
- A "tsarkake" wani na nufin a ware mutum domin aikin Yahweh.
Shawarwarin Fassara:
- Hanyoyin fassara "a ware daban" kan haɗa da " zaɓe na musamman" ko "warewa daga gare ka" ko a "ɗauki wani ɓangaren domin wani aiki na musamman".
- A "ware daban" za a iya fassara shi a kamar " iya warewa (daga)" ko " a iya zaɓenka na musamman."
(Hakanan duba: tsarki, tsarkakewa, zaɓe)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Afisawa 03: 17-19
- Fitowa 31:12-15
- Littafin Alƙalai 17:12
- Littafin Lissafi 03: 11-13
- Filibiyawa 01:1-2
- Romawa 01:01