1.3 KiB
1.3 KiB
tsarkake, a tsarkake, tsarkakewa
Ma'ana
A tsarkake na nufin a keɓe ko a maishe da tsarki. Tsarkakewa shi ne yadda ake maishe wa da tsarki.
- A Tsohon Alƙawari, wasu mutane da abubuwa an tsarkake su, ko a keɓe, domin hidima ga Allah.
- Sabon Alƙawari na koyarwa cewa Allah ya tsarkake mutane waɗanda suka bada gaskiya ga Yesu. Wato, ya maishesu masu tsarki ya kuma keɓe su domin su yi masa sujada.
- Masu bada gaskiya ga Yesu an dokace su da su tsarkake kansu ga Allah, su zama da tsarki cikin dukkan abin da suke yi.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta ga nassin, kalmar "tsarkake" za a iya fassarawa haka "a keɓe" ko "a maida da tsarki" ko "a tsarkake."
- Sa'ad da mutane suka tsarkake kansu, sun tsarkake kansu kuma sun bada kansu ga hidimar Allah. Yawanci kalmar "keɓewa" a cikin Littafi Mai Tsarki ana amfani da ita da wannan manufar.
- Sa'ad da ma'anar ta zama "keɓewa," wannan kalma za a iya fassarawa haka "a keɓe wani (ko wani abu) ga hidimar Allah."
- Ya danganta da nassin, faɗar "tsarkakewarka" za a iya fassarawa "sanya ka tsarkaka" ko "keɓe ka (domin Allah)" ko "abin da zai sa ka yi tsarki."
(Hakanan duba: tsarkakke, mai tsarki, keɓaɓɓe)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tasalonikawa 04:3-6
- 2 Tasalonikawa 02:13
- Farawa 02:1-3
- Luka 11:2
- Matiyu 06:8-10