920 B
920 B
Ba'sadusi, Sadusiyawa
Ma'ana
Sadusiyawa 'yan ƙungiyar siyasa ne na firistocin Yahudawa a zamanin Yesu Almasihu. Sun yadda da shugabancin Romawa basu kuma yadda akwai tashin matattu ba.
- Dayawa daga cikin Sadusiyawa masu dukiya ne, mawadata ne cikin Yahudawa waɗanda ke riƙe da matsayi na shugabanci masu daraja kamar shugaban firist da babban firist.
- Ayyukan Sadusiyawa ya kunshi kula da harabar haikali da kuma ayyukan firistoci kamar miƙa hadayu na baiko.
- Sadusiyawa da Farisiyawa sun zuga shugabannin Romawa domin su gicciye Yesu.
- Yesu ya yi magana gãba da waɗannan ƙungiyoyin addini domin son zuciyarsu da kuma munafuncinsu.
(Hakanan duba: shugabannin firistoci, majalisa, babban firist, munafuki, shugaban Yahudawa, Farisi, firist)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 04:03
- Ayyukan Manzanni 05:17-18
- Luka 20:27
- Matiyu 03:07
- Matiyu 16:01
- Matiyu 16:01