1.3 KiB
1.3 KiB
Asabaci
Ma'ana
Kalmar "Asabaci" na nufin rana ta bakwai cikin mako, wadda Allah ya dokaci Isra'ilawa da su keɓe ta ranar hutu kada a yi wani aiki.
- Bayan Allah ya gama hallitar duniya cikin kwana shida, sai ya huta a rana ta bakwai. Haka kuma, Allah ya dokaci Isra'ilawa da su keɓe rana ta bakwai a matsayin rana ta musamman don hutu da kuma yi masa sujada.
- Dokar "a kiyaye ranar Asabaci da tsarki" na ɗaya daga cikin dokoki goma da Allah ya rubuta kan allon dutsen da ya baiwa Musa domin Isra'ilawa.
- Bisa ga ƙidayar ranakun Yahudawa, ranar Asabaci daga faɗuwar ranar Jumma'a ne har zuwa Sati faɗuwar rana.
- Wani lokacin a cikin Littafi Mai Tsarki Asabaci ana kiranta "Ranar Asabaci" a maimakon Asabaci.
Shawarwarin Fassara:
- Wannan za a kuma iya fassarawa haka, "ranar hutawa" ko "ranar da ba a aiki" ko "ranar Allah ta hutawa."
- Wasu juyin na amfani da manyan haruffa wajen rubuta wannan kalma domin a nuna rana ce ta musamman, kamar "Ranar Asabaci" ko "Ranar Hutawa."
- Ayi la'akari da yadda ake fassara kalmar a yaren lardin ko na ƙasar.
(Duba kuma: hutu)
Wurarenda ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Tarihi 31:2-3
- Ayyukan Manzanni 13:26-27
- Fitowa 31:14
- Ishaya 56:6-7
- Littafin Makoki 02:06
- Lebitikus 19:03
- Luka 13:14
- Markus 02:27
- Matiyu 12:02
- Nehemiya 10:32-33