1.4 KiB
1.4 KiB
bayyanawa, ana bayyanawa, bayyananne, ruya ko wahayi
Ma'ana
kalmar "bayyanawa" na manufar a sa wani abu shi zama sananne. "Ruya" wani abin da aka sa aka san da shi ne.
- Allah ya sa an san da shi ta wurin dukkan abubuwan da ya hallita da kuma ta wurin sadarwasa da mutanensa ta wurin magana da kuma saƙonnai a rubuce.
- Allah yana bayyana kan sa kuma ta wurin mafalkai da wahayai.
- Da Bulus ya ce ya karɓa Labarin nan Mai Daɗi ta "ruya daga Yesu Kristi," yana nufi da cewa Yesu ne da kansa ya yi masa bayanin Labarin Mai Daɗi.
- A cikin littafin Sabuwar Alƙawari "Wahayi" Allah ke bayyana yanayin da zasu faru a kwanakin ƙarshe. Ya bayyana su ga ManzoYohanna ta wurin wahayi.
Shawarwarin Fassara:
- Wasu hanyoyin fassara "bayyanawa" zasu iya haɗawa da "asa ya zama sananne" ko "a buɗe" ko "a nuna a sarari."
- Ya danganta da nassin, wasu hanyoyin fassara "ruya ko wahayi" zai iya zama magana daga Allah" ko "abubuwan da Allah ya bayyana
ko "koye-koye game da Allah." zaifi kyau a riƙe ma'anar "bayyanawa" a cikin fassarar.
- Faɗar "inda babu ruya ko wahayi" za a iya fassarawa haka "sa'ad da Allah baya bayyana kansa ga mutane" ko "cikin mutane waɗanda Allah baiyi magana ba."
(Hakanan duba: labari mai daɗi, mafarki, wahayi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Daniyel 11:1-2
- Afisawa 03:05
- Galatiyawa 01:12
- Littafin Makoki 02:13-14
- Matiyu 10:26
- Filibiyawa 03:15
- Wahayin Yahaya 01:01