1.2 KiB
1.2 KiB
a tuba, tube-tube, tubabbe, tuba
Ma'ana
Kalmomin "a tuba" da "tuba" na nuna juyawa daga barin zunubi a kuma juya ga Allah.
- A "tuba" na nufin wani ya canza tunanin zuciyarsa.
- A Littafi Mai Tsarki, "tuba" na nufin a juyo daga tunani da ayyuka na mutuntaka na zunubi, a kuma juyo zuwa ga tunani da ayyukan Allah.
- Yayin da mutane suka tuba daga zunubansu, Allah na gafarta masu ya kuma taimaka masu su fara yi masa biyayya.
Shawarwarin Fassara:
- Kalmar "tuba" za a iya fassarawa da kalma ko faɗa dake ma'anar "juyawa (ga Allah)" ko "juyawa daga zunubi zuwa kuma ga Allah" ko "juyawa zuwa ga Allah, nesa da zunubi."
- Yawanci kalmar "tuba" za a iya fassarawa da amfani da aikatawa "ka tuba." Ga misali, "Allah ya bayar da tuba ga Isra'ila" za a iya fassarawa haka "Allah ya ba Isra'ila ikon su tuba."
- Wasu hanyoyin da za a fassara "tuba" zasu haɗa da "juyawa daga zunubi" ko "juyawa ga Allah kuma nesa da zunubi."
(Hakanan duba: gafartawa, zunubi, juyawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 03:19-20
- Luka 03:3
- Luka 03:8
- Luka 05:32
- Luka 24:47
- Markus 01:14-15
- Matiyu 03:03
- Matiyu 03:11
- Matiyu 04:17
- Romawa 02:04