1.0 KiB
1.0 KiB
ringi
Ma'ana
Kalmar "ringi" fassara kai tsaye na manufar "sauran da suka rage" ko na mutane ko na wani abu daga masu yawa.
- Yawancin lokatai "ringi" na nuna ragowar mutane ne waɗanda suka rayu daga cikin matsalar rayuwa ko suka yi tsayaya cikin aminci ga Allah yayin da suke fuskantar tsanani.
- Ishaya ya yi magana game da ragowar Yahudawan da zasu rage sun tsira daga hare-haren bãƙi su kuma dawo ga Ƙasar Alƙawari a Kana"an.
- Manzo Bulus ya yi magana game da "ringi" mutanen da Allah ya zaɓa da zasu karɓi alherinsa.
- Kalmar nuna "ringi" mutanen da basu yi aminci ba ko basu rayu ba ko ba a zaɓe su ba.
Shawarwarin Fassara:
- Faɗa kamar haka "ringin mutanen nan" za a iya fassarawa haka "sauran mutanen nan" ko "mutanen da suka rage amintattu" ko "mutanen da aka bari."
- "Dukkan ringin mutanen" za a iya fassarawa ta haka " dukkan sauran mutanen" ko "mutanen da suka rage."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 15:17
- Amos 09:12
- Ezekiyel 06:8-10
- Farawa 45:07
- Ishaya 11:11
- Mika 04:6-8