774 B
774 B
zabura, zaburai
Ma'ana
Wannan magana "zabura" na nufin keɓaɓɓun waƙoƙi, yawancin lokaci an rubuta su kamar haddace da za a raira.
- Littafin Tsohon Alƙawari na Zabura nada tarin waɗannan waƙoƙi waɗanda Sarki Dauda ya rubuta da wasu Isra'ilawa kamar su Musa, Suleman, da Asaf, da dai sauransu.
- Al'ummar Isra'ila sun yi amfani da waɗannan zaburan a cikin sujadarsu ga Allah.
- Za a iya amfani da zabura a bayyana murna, bangaskiya, da girmamawa, da kuma ciwo da baƙinciki.
- A cikin Sabon Alƙawari, an gargaɗemu muyi waƙoƙin zabura ga Allah a matsayin yi masa sujada.
(Hakanan: Dauda, bangaskiya, murna, Musa, tsarki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 13:33
- Ayyukan Manzanni 13:35
- Kolosiyawa 03:16
- Luka 20:42