ha_tw/bible/kt/promisedland.md

1.2 KiB
Raw Permalink Blame History

Ƙasar Alƙawari

Ma'ana

Wannan furci Ƙasar Alƙawari yana cikin labarun Littafi Mai Tsarki amma ba cikin nassin Littafi Mai Tsarki yake ba. Wata hanya ce ta bayyana ƙasar Kan'ana da Allah ya rigaya ya alƙawarta wa Ibrahim da zuriyarsa.

  • lokacin da Ibrahim yake zaune a cikin birnin Ur, Allah ya umarce shi ya tafi ya zauna cikin ƙasar Kan'ana. Shi da zuriyarsa, Isra'ilawa sun zauna a can shekaru da yawa.
  • Lokacin da aka yi fari, wannan babbar yunwa ta sa babu abinci a Kan'ana, Isra'ilawa suka tafi zuwa Masar.
  • Bayan shekaru ɗari huɗu, Allah ya kuɓutar da Isra'ilawa daga bauta a Masar ya kuma sake dawo da su Kan'ana, ƙasar da Allah ya yi alƙawari zai basu.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana "Ƙasar Alƙawari" za a iya fassarawa haka, "ƙasar da Allah yace zai bayar ga Ibrahim" ko "ƙasar da Allah ya alƙawarta wa Ibrahim" ko "ƙasar da Allah ya alƙawarta wa mutanensa" ko "ƙasar Kan'anan."
  • A cikin nassin Littafi Mai Tsarki, wannan sunan wuri an faɗe shi haka, "ƙasar da Allah ya alƙawarta."

(Hakanan duba: Kan'ana, alƙawari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 08:1-2
  • Ezekiyel 07:26-27