2.3 KiB
2.3 KiB
firist, firistoci, firistanci
Ma'ana
A cikin Littafi Mai Tsarki, firist mutum ne wanda aka zaɓa domin ya miƙa hadayu ga Allah a saboda mutanen Allah. "Matsayin firistoci" sunan aiki ne ko zama firist.
- A cikin Tsohon Alƙawari, Allah ya zaɓi Haruna da zuriyarsa su zama firistocinsa domin mutanen Isra'ila.
- "Masayin firist" hakki ne kuma nawaya ce da aka miƙa daga mahaifi zuwa ga ɗa cikin iyalin Lebiyawa.
- Firistocin Isra'ila suna da nawayar miƙa hadayun mutane ga Allah, kuma da waɗansu ayyuka a cikin haikali.
- Firistoci kuma suna miƙa addu'o'i ga Allah akai akai domin mutane suna kuma yin wasu ayyukan addini da suka wajaba a cikin haikali.
- Firistoci sukan furta albarku akan mutane su kuma koya masu dokokin Allah.
- A lokacin Yesu, akwai matsayin firistoci hawa hawa, har ma da manyan firistoci da kuma babban firist.
- Yesu shi ne namu "babban firist mai girma" wanda yake roƙo domin mu a gaban Allah. Ya miƙa kansa hadaya mafificiya domin zunubi. Wannan ya nuna cewa hadayu da firistoci 'yan adam suke miƙawa ba a buƙatar su kuma.
- A cikin Sabon Alƙawari, kowanne mai bada gaskiya ga Yesu ana kiransa "firist" zai iya zuwa kai tsaye gun Allah cikin addu'a ya yi roƙo domin kansa da kuma wasu mutane.
- A zamanin dã, akwai firistoci matsafa dake miƙa baye-baye ga gumaku kamar su Ba'al.
Shawarwarin Fassara:
- Zai danganta ga nassi, wannan magana "firist" za a iya fassarawa haka, "mutumin dake miƙa hadaya" ko "matsakanci na Allah" ko "matsakanci mai hadaya" ko " mutumin da Allah ya naɗa ya wakilce shi."
- Fassara kalmar nan "firist" zai zama daban da "matsakanci."
- Wasu juyin watakila sun fi son koyaushe su ce "firistocin Isra'ila" ko "firistocin Yahudawa" ko "firist ɗin Yahweh" ko "firist ɗin Ba'al" domin a fayyace da kyau ba wai ana nufin i firistoci irin na wannan zamani a yau ba.
- Maganar da aka yi amfani da ita a fassara "firist" yakamata ta banbanta da wannan magana "shugaba firist" da "babban firist" da "Lebiyawa" da "annabi."
(Hakanan duba: Haruna, manyan firistoci, babban firist, matsakanci, hadaya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Tarihi 06:41
- Farawa 14:17-18
- Farawa 47:22
- Yahaya 01:19-21
- Luka 10:31
- Markus 01:44
- Markus 02:25-26
- Matiyu 08:4
- Matiyu 12:04
- Mika 03:9-11
- Nehemiya 10:28-29
- Nehemiya 10:34-36
- Wahayin Yahaya 01:06