974 B
974 B
ƙaddara, an ƙaddara
Ma'ana
Wannan kalma "ƙaddara" manufarta shi ne yanke shari'a ko shiryawa cewa wani abu zai faru.
- Wannan magana masamman akan Allah ne mai ƙaddara wa mutane su karɓi rai madawwami."
- Wani lokaci kalmar nan "rigasaninsa" ana amfani da ita wanda ma'anarta ita ma yanke shari'a kafin abu ya faru ne.
Shawarwarin Fassara:
- Wannan kalma "ƙaddara" za a iya fassarawa haka, "yanke shari'a kafin" ko "yanke shari'a tun gabannin lokaci."
- Wannan kalma "ƙaddara" za a iya fassarawa haka, "yanke shari'a tun dã dã" ko "shirin da aka yi tun gabannin lokaci." ko "yanke shari'a tun kafin."
- Furci kamar haka "an ƙaddara mu" za a iya fassarawa haka, "ya yanke shari'a tun dã dã cewa mu" ko "ya rigaya ya yanke shari'a tun gabannin lokaci cewa mu."
- A yi lura domin fassarar wannan kalmar ta bambanta da fassarar wannan kalmar "rigasani."
(Hakanan duba: rigasani)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korintiyawa 02:6-7