1008 B
1008 B
hallaka, hallakarwa, lalacewa
Ma'ana
Wannan kalma "hallaka" ma'anarta shi ne mutuwa ko lalatarwa, yawancin lokaci haka takan faru ne da ƙarfi da yaji ko kuma wani bala'i. A cikin Littafi Mai Tsarki, wannan kalma nada ma'ana musamman ta hukunci na har abada a wutar lahira.
- Mutanen dake "hallaka" sune waɗanda an ƙaddara su ga wutar lahira domin sun ƙi su bada gaskiya ga Yesu domin cetonsu.
- Yahaya 3:16 ya koyar da cewa "hallaka" shi ne rashin kasancewa har abada a sama.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta ga nassi, hanyoyin fassara wannan magana za a haɗa da waɗannan, "mutuwa ta har abada" ko "a hukunta a lahira ta wuta" ko "a lalatar."
- A tabbata fassarar "hallaka" ta bada ma'anar kasancewa a wutar lahira har abada ba wai kuma mutumin nan "bashi da rai ne ba."
(Hakanan duba: mutuwa, har abada)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Bitrus 01:23
- 2 Korintiyawa 02:16-17
- 2 Tasalonikawa 02:10
- Irmiya 18:18
- Zabura 049:18-20
- Zakariya 09:5-7
- Zakariya 13:08