ha_tw/bible/kt/passover.md

1.3 KiB
Raw Permalink Blame History

Idin Ƙetarewa

Ma'ana

"Idin Ƙetarewa" sunan wani idi ne na addini wanda Yahudawa suke bikinsa kowacce shekara, domin su tuna da yadda Allah ya kuɓutar da kakanninsu, Isra'ilawa, daga bauta a ƙasar Masar.

  • Sunan wannan buki ya zo daga lokacin da Allah ya "Ƙetare" gidajen Isra'ilawa bai kashe 'ya'yansu maza ba sa'ad da ya kashe 'ya'yan fari maza na Masarwa.
  • Wannan bukin Ƙetarewar ya haɗa da cin musamman abinci na naman ɗan rago da aka kashe aka gasa da kuma gurasa marar gami. Waɗannan cimar suna tunashe su kan abincin da Isra'ilawa suka ci a daren da zasu kubce daga Masar.
  • Allah ya gaya wa Isra'ilawa su ci wannan abinci kowace shekara domin su tuna da yadda Allah ya "Ƙetare" gidajensu da yadda ya baratar dasu daga bautar Masar.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan furci "Ƙetarewa" za a iya fassara shi ta wurin haɗa waɗannan kalmomin "Idi" da "Ƙetarewa." ko kuma haɗin wasu kalmomi da suke da wannan ma'ana.
  • Zai taimaka idan sunan wannan buki yana da kalmomin da suka faɗi yadda mala'ikan Ubangiji ya tsallake gidajen Isra'ilawa ya bar 'ya'yansu maza da rai.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 05:07
  • 2 Tarihi 30:13-15
  • 2 Sarakuna 23:23
  • Maimaitawar Shari'a 16:02
  • Fitowa 12:26-28
  • Ezra 06:21-22
  • Yahaya 13:01
  • Yoshuwa 05:10-11
  • Lebitikus 23:4-6
  • Littafin Lissafi 09:03