640 B
640 B
ƙaron mur
Ma'ana
Ƙaron Mur wani irin mai ne ko kayan ƙanshi da ake yinsa daga ƙaron itacen mur dake yaɗuwa a sa a Afrika da Asiya. Yana kama da turaren ƙaron frank.
- Ana amfani da mur domin ayi kayan ƙamshi, turare, da magani da kuma shirya gawawwaki domin biznewa.
- Mur yana ɗaya daga cikin kyautai da masana suka ba Yesu da aka haife shi.
- An miƙa wa Yesu ruwan inabi gauraye da mur don a sauƙaƙe wa Yesu zafin azaba da aka giciye shi.
(Hakanan duba: turaren ƙaron frank, masana)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Fitowa 30:22-25
- Farawa 37:25-26
- Yahaya 11:1-2
- Markus 15:23
- Matiyu 02:11-12