1.2 KiB
1.2 KiB
jinƙai, mai jinƙai
Ma'ana
Waɗannan maganganu "jinƙai" da "mai jinƙai" ana nufin taimaka wa mutane ne waɗanda ke da buƙata, musamman sa'ad da suke cikin yanayin kasawa da ƙasƙanci.
- Wannan kalmar "jinƙai" ma'anarta fasa hukunta mutane saboda laifinsu ya ƙunshi ma'anar ƙin hukunta mutane don wani abin da basu yi dai-dai ba.
- Mutum mai iko kamar sarki za a ce yana da "jinƙai" sa'ad da ya yi wa mutane alheri maimakon mugunta.
- Nuna jinƙai shi ne lokacin da muka taimaki wani mutum da ya yi mana laifi.
- Mukan nuna jinƙai sa'ad da muka taimaki mutanen da suke cikin buƙata mai
tsanani.
- Allah yana mana jinƙai, yana so mu kuma mu yiwa wasu jinƙai.
Shawarwarin Fassara
- Yadangana ga nassi, za a iya fassara "jinƙai" a ce "alheri" ko "juyayi" ko "tausai."
- Wannan magana "jinƙai" za a iya fassara ta haka "nuna tausai" ko "yin alheri ga" ko "gafartawa."
- "Nuna jinƙai ga" ko "yin jinƙai ga" za a iya fassarawa haka "yin kirki" ko "yin jinƙai ga."
(Hakanan duba: juyayi, gafartawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Bitrus 01:3-5
- 1 Timoti 01:13
- Daniyel 0:17
- Fitowa 34:06
- Farawa 19:16
- Ibraniyawa 10:28-29
- Yakubu 02:13
- Luka 06:35-37
- Matiyu 09:27
- Filibiyawa 02:25-27
- Zabura 041:4-6
- Romawa 12:01