1.0 KiB
1.0 KiB
manna
Ma'ana
Manna wata farar, ƙwayar abinci ce da Allah ya tanada wa Isra'ilawa su ci lokacin kasancewarsu shekara 40 a jeji bayan sun baro Masar.
- Manna tayi kama da farar waina mai faɗowa kowacce safiya a ƙasa ƙarƙashin raɓa. Tana da zaƙi, kamar zuma.
- Isra'ilawa sukan tara wainar manna kowacce rana amma banda ranar Asabaci.
- A ranar kafin Asabaci, Allah ya gayawa Isra'ilawa su tattara riɓi biyu na manna domin kada su fita tara ta a ranar hutawarsu.
- Wannan kalma "manna" ma'anarta "Mene ne wannan?"
- A cikin Littafi Mai Tsarki, a kan ce da ita "waina daga sama" da "kwaya daga sama."
Shawarwarin Fassara:
- Wasu hanyoyin fassara wannan magana za a iya cewa "wani siririn abinci fari" ko "abinci daga sama."
- Kuma a duba yadda aka fassara wannan kalmar a cikin Littafi Mai tsarki a cikin wani harshen ƙasar.
(Hakanan duba: waina, jeji, ƙwayar, sama, Asabaci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Maimaitawar Shari'a 08:3
- Fitowa 16:27
- Ibraniyawa 09:3-5
- Yahaya 06:30-31
- Yoshuwa 05:12