826 B
826 B
ranar hukunci
Ma'ana
Kalmar "ranar hukunci" na nufin wani lokaci a nan gaba sa'ad da Allah zai shar'anta kowanne taliki.
- Allah ya sanya ɗansa, Yesu Almasihu, alƙalin dukkan mutane.
- A ranar hukunci, Almasihu zai hukunta mutane bisa ga ɗabi'arsa ta adalci.
Shawarwarin Fassara:
- Ana iya fassara wannan kalma "lokacin hukunci" tunda yana nufin fiye da rana ɗaya.
- Sauran hanyoyin fassara wannan kalma na iya haɗawa da "ƙarshen zamani sa'ad da Allah zai hukunta dukkan mutane."
- Wasu fassarorin na dasa wa akan wannan kalma suna nuna cewa sunan wata rana ce ko lokaci na musamman:" "Ranar hukunci" ko "Lokacin Hukunci."
(Hakanan duba: alƙali, Yesu, sama, lahira)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Luka 10:12
- Luka 11:31
- Luka 11:32
- Matiyu 10:14-15
- Matiyu 12:36-37
- Matiyu 12:36-37