830 B
830 B
Bayahude, Yahudanci, Yahudawa
Ma'ana
Yahudawa mutane ne zuriyar Yakubu jikan Ibrahim. Kalmar "Bayahude" ta fito daga kalmar "Yahuda."
- Mutane ne suka fara kiran Isra'ilawa "Yahudawa" bayan da suka dawo Yahuda daga hijira a Babila.
- Yesu wanda yake shine Mesaya Bayahude ne. Duk da haka, shugabannin addinin Yahudanci suka ƙi Yesu suka kuma nemi cewa a kashe shi.
- Yawancin lokaci furta kalmar "Yahudawa" ana nufin shugabannin Yahudawa, ba dukkan mutane Yahudawa ba. A cikin wannan rukunin, wurin fassarar kalmar wasu suna haɗawa da "shugabannin" domin a ƙara fahimta.
(Hakanan duba: Ibrahim, Yakubu, Isra'ila, Babila, shugabannin Yahudanci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan manzanni 02:05
- Ayyukan manzanni 10:28
- Ayyukan manzanni 14:5-7
- Kolosiyawa 03:11
- Yahaya 02:14
- Matiyu 28:15