1.2 KiB
1.2 KiB
roƙo a madadi, yin roƙo a madadi, aikin yin roƙo a madadi
Ma'ana
Kalmomin nan "roƙo" da "yin roƙo" na nufin yin roƙo domin wani ko a madadin wani mutum. A cikin Littafi Mai Tsarki harkullum wannan na nufin yin addu'a domin waɗansu mutane.
- Maganan nan "yin roƙo domin" da kuma "tsaya wa a tsakani domin" yana nufin yin roƙo ga Allah domin amfanin sauran mutane.
- Littafi Mai Tsarki na koyar da mu Ruhu Mai Tsarki na yin addu'a domin mu, Yana addu'a zuwa ga Allah domin mu.
- Mutumin da ke roƙo domin sauran mutane ta wurin kai roƙonsu ga wata hukuma kowani mai mulki.
Shawarwarin Fassara:
- Waɗansu hanyoyi na fassara "roƙo a madadi" zai haɗa da "yin roƙo domin" ko "roƙon wani domin ya yi wani abu domin (wani)."
- Kalmar nan ana fassara ta da yin "koke" ko "roƙo" ko "addu'a ta matsananciyar bukata."
- Kalmar nan "yin addu'a domin" za'a iya fassara ta "yin roƙo domin amfanin waɗansu" ko "yin koke a madadin" ko "roƙon Allah domin ya taimaki wani" ko "roƙon Allah ya albarkaci (wani)."
(Hakanan duba: addu'a)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ibraniyawa 07:25-26
- Ishaya 53:12
- Irmiya 29:6-7
- Romawa 08:26-27
- Romawa 08:33-34