1.2 KiB
1.2 KiB
munafuki, munafunci, halin munafunci
Ma'ana
Kalmar nan "munafiki" tana nufin mutum wanda ke yin abubuwan da ke kamar na adalci a ganin ido, amma a asirce yana yin miyagun ayuka. Kalmar halin "munafunci" na nufin halin da ke yaudarar mutane inda suke tunanin mutumin adali ne.
- Munafuki na son yin abubuwa da mutane zasu yi tunanin nagari ne.
- Sau da yawa munafukai kan dinga ganin kuskuren sauran mutane sabo da suna yin wannan abin da su da kansu suke aikatawa.
- Yesu ya kira Farisiyawa munafukai sabo da duk da yake suna yin ayukan addini, kamar sa waɗansu suturu da cin wani irin abinci, amma basu da kirka ga sauran mutane.
- Munafuki kan ga laifin sauran mutane, amma shi bai karɓar nasa kurakuran.
Shawarwarin Fassara:
- Waɗansu harsuna na da kalma kamar "fuska biyu" wannan na nufin aiki munafuki.
- Waɗansu hanyoyi na yin fassara "munafuki" sun haɗa da "fankama" ko "aikin ganin ido" ko "ɗaga kai, mayaudarin mutum."
- Kalmar "halin munafunci" za'a iya fassara ta da "yaudara" ko "yin ayuka na jabu" ko "na ganin ido."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Galatiyawa 02:13
- Luka 06:41-42
- Luka 12:54-56
- Luka 13:15
- Markus 07:6-7
- Matiyu 06:1-2
- Romawa 12:9