1010 B
1010 B
tawali'u, yin tawali'u, ƙasƙantarwa, halin tawali'u
Ma'ana
Kalmar nan "tawali'u" na bayyana mutum wanda baya ɗaukan kansa cewa ya fi wani. Bai da da girman kai ko fahariya. Tawali'u shi ne a zama da hali na rashin ɗaga kai.
- Zama da tawali'u a gaban Allah na nufin mutun ya gane kasawarsa da rashin cikarsa in an kwatanta da girmansa, hikimarsa, cikarsa.
- Lokacin da mutum ya zama da tawali'u ya sa kansa a ƙaramin matsayi.
- Halin tawali'u shi ne kula da bukatun sauran mutane fiye da bukatun mutum.
- Hakanan halin tawali'u na nufin yin hidima da nuna gurbin da ya kamata a lokacin da mutum ke moron baiwarsa.
- Batun nan "zama mai mai tawali'u" za'a iya fassara shi da "kada ka nuna girman kai."
- "Ku zama da tawali'u a gaban Allah" za'a iya fassara ta da "Ku miƙa nufinku ga Allah, ku yi la'akari da girmansa."
(Hakanan duba: girman kai)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Yakubu 01:21
- Yakubu 03:13
- Yakubu 04:10
- Luka 14:11
- Luka 18:14
- Matiyu 18:04
- Matiyu 23:12