26 lines
1.4 KiB
Markdown
26 lines
1.4 KiB
Markdown
|
# Yoshuwa
|
||
|
|
||
|
## Gaskiya
|
||
|
|
||
|
Akwai mutane Isra'ilawa da yawa masu suna Yoshuwa a cikin Littafi Mai tsarki. Wanda aka fi sani shine Yoshuwa ɗan Nun mataimakin Musa wanda kuma daga bisani ya zama muhimmin shugaba na mutanen Allah.
|
||
|
|
||
|
* Yoshuwa na ɗaya daga cikin 'yan leƙen asirin ƙasa da Musa ya aika su tafi binciken ƙasar Alƙawari.
|
||
|
* Tare da Kaleb, Yoshuwa ya roƙi mutanen Isra'ilawa da suyi biyayya da umarnin Allah su shiga Ƙasar Alƙawari su kayar da Kan'aniyawa.
|
||
|
* Shekaru da yawa daga bisani, bayan mutuwar Musa, Allah ya zaɓi Yoshuwa ya bida mutanen Isra'ila zuwa Ƙasar Alƙawari.
|
||
|
* A yaƙi na farko kuma wanda aka fi sani gãba da Kan'aniyawa, Yoshuwa ya bida Isra'ilawa suka kayar da birnin Yeriko.
|
||
|
* Littafin Yoshuwa a Tsohon Alƙawari ya faɗi yadda Yoshuwa ya bida Isra'ilawa suka ɗauki mallakar Ƙasar Alƙawari da yadda kuma ya ba kowacce kabilar Isra'ila fannin ƙasar domin su zauna.
|
||
|
* An kuma ambaci Yoshuwa ɗan Yozadak a cikin litattafan Haggai da Zakariya; shi baban firist ne wanda ya taimaka aka sake gina ganuwoyin Urshalima.
|
||
|
* Akwai kuma mutane da yawa masu suna Yoshuwa da aka ambata a cikin tarihohin asali da saura wurare a Littafi Mai Tsarki.
|
||
|
|
||
|
|
||
|
(Hakanan duba: Kan'ana, Haggai, Yeriko, Musa, Ƙasar Alƙawari, Zakariya (Tsohon Alƙawari))
|
||
|
|
||
|
|
||
|
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
|
||
|
|
||
|
* 1 Tarihi 07:25-27
|
||
|
* Maimaitawar Shari'a 03:21
|
||
|
* Fitowa 17:10
|
||
|
* Yoshuwa 01:03
|
||
|
* Littafin Lissafi 27:19
|