27 lines
1.0 KiB
Markdown
27 lines
1.0 KiB
Markdown
|
# sasantawa, an sasanta, sasantuwa, sulhu, sulhunta
|
||
|
|
||
|
## Ma'ana
|
||
|
|
||
|
A "sasanta" da kuma "sasantawa" na nufin "yin sulhu" tsakanin mutanen da can baya maƙiyan juna ne. "Sasantawa" ayyuka ne na yin sulhu.
|
||
|
|
||
|
* A Littafi Mai Tsarki, wannan kalmar na nuna yadda Allah ke sulhunta mutane zuwa gare shi ta wurin Ɗansa, Yesu Almasihu.
|
||
|
* Saboda zunubi, dukkan mutane sun zama maƙiyan Allah. Amma saboda ƙaunarsa mai girma, Allah ya yi tanadin hanya domin mutane a sasanta su ta wurin Yesu.
|
||
|
* Ta wurin yarda da hadayar da Yesu ya yi domin biyan fansar zunubansu, mutane zasu iya gafartawa su kuma sami salama da Allah.
|
||
|
|
||
|
|
||
|
Shawarwarin Fassara:
|
||
|
|
||
|
* Kalmar "sulhu" za a iya fassarawa haka "a kawo salama" ko "a maido da kyakkyawan zumunci" ko "a sa a zama abokai."
|
||
|
* Kalmar "sulhuntawa" za a iya fassarawa haka "maido da kyakkyawan zumunci" ko "sanya salama" ko "a haddasa zumunci mai salama."
|
||
|
|
||
|
|
||
|
(Hakanan duba: salama, hadaya)
|
||
|
|
||
|
|
||
|
Wuraren ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
|
||
|
|
||
|
* 2 Korintiyawa 05:19
|
||
|
* Kolosiyawa 01:18-20
|
||
|
* Littafin Misalai 13:17-18
|
||
|
* Romawa 05:10
|