ha_tw/bible/names/annas.md

18 lines
788 B
Markdown
Raw Permalink Normal View History

2021-06-08 22:05:51 +00:00
# Anas
## Gaskiya
Anas babban firist ne na Yahudawa a Yerusalem na tsawon shekara 10, daga AD 6 zuwa AD 15. Sa'an nan gwamnatin Romawa ta cire shi daga matsayin manyan firistoci, koda shi ke ya ci gaba da zama tsayayyen shugaba a cikin Yahudawa.
* Anas surikin Kefas ne, zaɓaɓɓen babban firist a lokacin hidimar Yesu.
* Bayan manyan firistoci sun yi murabus, sukan riƙe sunan muƙaminsu tare da wasu ayyukan hidima na matsayinsu. Saboda haka ne ake ce da Anas babban firist a zamanin firistancin Kefas da waɗansu.
* A lokacin da ake shar'anta shi a gaban shugabannin Yahudawa, an kawo Yesu da fari a gaban Anas domin ayi masa tambayoyi.
(Hakanan duba: babban firist, firist)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 04:5-7
* Yahaya 18:22-24
* Luka 03:02