Ta wace hanya ce Allah ya yi alkawarin bishara kafin lokacin Bulus?
Allah ya yi alkawarin bishara a dă kafin annabawa a cikin littafi mai tsarki.
Da ga wani zuriya ne bisa ga jiki aka haife Ɗan Allah?
An haife Ɗan Allah a zuriyar Dauda ne bisa ga jiki.