ha_tq/psa/62/09.md

416 B

Yaya Dauda ya kwatanta waɗanda ke tsaye ƙassa da sama?

Ba shakka mutanen da basu da matsayi ba komai bane, waɗanda ke da matsayin kuma ƙarya ne. Idan a ka auna su a ma'auni ba su da nauyi, inda za a haɗa su a auna ba su da nauyin komai.

A kan mene ne Dauda yace mutane kada su sa zuciyarsu?

Yace kada ku dogara ga aikin zalunci ko ƙwace, kada ku sa begenku ga dukiyar wofi, gama ba su da amfanin komai.