ha_tq/mat/23/34.md

529 B

Menene Yesu ya ce marubuta da Farisawa za su yi wa annabawa, masu hikima da marubuta da zai aike su?

Yesu ya ce za su ƙashe wasu su kuma gicciye wasu, su bulale wasu, a kuma kore wasu daga gari zuwa gari.

Bisa ga sakamakon halinsu, wane alhakin laifi ne zai sauko wa marubuta da Farisawa?

Alhakin jinin dukkan adalai da aka zubar a duniya zai sauko kan marubuta da Farisawa.

Ga wane zamani ne Yesu ya ce dukkan waɗannan abubuwa za su faru?

Yesu ya faɗa cewa ga wannan zamani ne dukkan waɗannan abubuwa za su faru.